Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Katsina, ta kama wasu mutane biyu da take zargi da safarar tabar wiwi bayan ta cafke su da kilo 7 na wasu haramtattun kayan maye.
A cewar Kwamandan hukumar Mohammed Bashir Ibrahim, yace, tuni hukumar ta gurfanar da wadanda take zargin a gaban kotu.
Katsina Post ta rahoto cewa, wadanda ake zargin Rabi Musa tare da mijin ‘yar uwarta, Suleiman Umar, an kama su ne a Sabon Titin Kwado da ke Unguwar Barhim a cikin birnin jihar Katsina.
Majiyar ta sake rahoto cewa, Rabi Musa tana taimaka ma mijinta mai suna Sani wanda a yanzu haka yake sana’ar sayar da kwayoyi.
Kwamandan NDLEA ya yi kira ga iyaye da su tabbatar an gudanar da gwajin gaskiya kan ta’ammuli da miyagun kwayoyi kafin daura aure tsakanin ‘ya’yansu mata da mazajen da suke son aurensu kamar yadda ake yi na gwajin kwayoyin halitta da sauran su.