A ranar Talata, 21 ga watan Yuni, 2022, sojojin runduna ta 13 da ke aiki karkashin runduna ta 82, sun tare wata mota kirar Toyota Camry mai lamba JAL 492 AA, dauke da alburusai iri-iri, a yayin da ta nufi kauyen Utanga zuwa tsaunin Obudu a jihar Kuros Riba.
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce dakarun da aka tura, Forward Operating Base Amana, sun yi yunkurin tsayar da motar a shingen bincikensu amma direban ya kauce wa binciken da aka yi masa ya kuma zarce. Direban ya yi haka ne don ya arce, inda sojojin suka bude wuta kan tayar motar.
- Sojoji Sun Tsinci Daya Daga Cikin Matan Chibok Da Boko Haram Suka Sace
- An Kashe ‘Yan Boko Haram 47 A Arangamarsu Da Sojoji A Borno
Wani kwakkwaran bincike da aka gudanar a kan motar, ya nuna cewa tana dauke da kaya masu fashewa 72, Dynamite Liquid 121, 200 na 7.62 mm (NATO) da harsashi 82 na 7.62 mm (na musanman). Sauran kayayyakin da aka gano a cikin motar da aka kama sun hada da kakin sojoji da kayan yaki.“Ana kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa sojojinmu da sahihan bayanai da za su kawo karshen matsalar rashin tsaro a fadin kasar nan,” in ji kakakin rundunar sojin.