Wani rahoto da kungiyar kula da tsare-tsaren shugabanci (PLSI) ta fitar, ya bayyana jihohin Kano, Borno da Benuwe a matsayin jihohi mafi karancin maki wajen bayyana rahoton yadda suka kashe kudaden gwamnati.
Rahoton mai taken binciken jihohi kan yadda suka tafiyar da dukiyar al’umma na shekarar 2022, ya nuna matakan nuna gaskiya da gwamnati ke bi wajen tafiyar da dukiyar al’umma a hukumance a duk fadin jihohi 36.
Rahoton wanda ya bayyana jihohin Akwa Ibom, Yobe da Katsina a matsayin wanda suka fi samun maki wajen bayyana kudaden da gwamnati ke kashewa, ya nuna cewa jihohi 21 ba su buga cikakken rahoton kudin da suka kashe ba na shekarar 2021 a yanar gizo, jihohi 19 kuma kwata-kwata ba su buga rahoton kudin ba na shekarar 2020.
Ya ce jihohi 10 ne kawai suka aiwatar da tanadin dokar kudi na babban ofishin tattara bayanan kudi yayin da jihohi 2 daga cikin 36 suna cigaba da kokarin tabbatar da tsarin ga babban ofishin.