Jiya Asabar 1 ga wata ne, aka kaddamar da taron shekara shekara na sadarwar latirori na kasar Sin karo na 16, da babban taron bayar da lambar yabo ta kungiyar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta shekarar 2023 a birnin Zhuhai na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, inda aka ba da lambar yabo na fara aikin watsa shirye-shiryen talabijin da fasahar 4K/8K na CMG.
Kungiyar fasahar latirorin kasar Sin ce ta shirya taron shekara shekara na sadarwar latirori na kasar karo na 16, mai taken “sabon zamanin latirori da sabon zangon ci gaban kasa”, wanda ya samu halartar masana da wakilan kamfanoni sama da 5000.
A sa’i daya kuma, an kira babban taron bayar da lambar yabo kan ci gaban kimiyya da fasaha na kungiyar latirorin kasar Sin na shekarar 2023, inda aka ba da lambobin yabo da yawansu ya kai 72 ga ayyukan ci gaban kimiyya da fasaha a bangaren latirori a shekarar 2021 zuwa 2022. (Mai fassarawa: Jamila)