Kwanan nan, Amurka ta tsara tare da gudanar da “taron kolin dimokuradiyya” karo na biyu. Duk da cewa a wannan karo, ta hada gwiwa da kasashen Koriya ta kudu da Netherlands da Zambia da ma Costa Rica wajen gudanar da taron, a yunkuri na kara abin da take kira wai “wakilci na dimokuradiyya”, amma ko ta yaya taron zai kasance abin dariya ne kawai.
Na farko, shi kansa wannan taro babu dimokuradiyya a cikinsa, kasancewar wadanda suka halarci taron ba sabo da son ransu ba ne, kana ba sabo da sun zama abin koyi wajen dimokuradiyya ba, amma sabo da Amurka ce ta zabe su. Wato ke nan ikon Amurka ne. Misali, duk da cewa Turkiyya da Hungary mambobin kungiyar NATO ne, amma ba su samu goron gayyata daga Amurka ba, sakamakon yadda suke yi mata rashin biyayya.
Na biyu kuwa, Amurka ta gudanar da taron ne ba don dimokuradiyya ba, kasancewar taron mataki ne da Amurka ta dauka don tada yakin cacar baka, wato tana saka wasu kasashe cikin wani rukuni da ma wasu cikin wani na daban, bisa ma’auninta na wai “dimokuradiyya”, don haifar da kiyayya a tsakaninsu.
Na uku, abin dariya ne yadda Amurka ta kasance mai kiran wannan taro, kasancewar kasar ta kawar da idonta daga matsalolin hakkin bil Adam da take fuskanta a cikin gida, inda ake ta fama da matsalolin wariyar launin fata da harbe-harben bindiga da dai makamantansu, kuma kwanaki biyu kafin taron, an sake jin karar bindiga a wata makaranta da ke jihar Tennesse, lamarin da ya kai ga halaka mutane da dama, amma ga shi shugaban Amurka ya halarci taron tamkar babu abin da ya faru ba. Baya ga haka, Amurka ta kuma yi ta lalata dimokuradiyya a waje, inda ta tilasta sauran kasashen duniya su yi na’am da ra’ayoyinta na dimokuradiyya, tare da nuna fin karfi, ga kuma munanan laifukan da ta aikata a kasashen Afghanistan da Iraki da Syria, amma kuma tana daukar kanta a matsayin mai koyar da dimokuradiyya a duniya.
Dimokuradiyya ba abin ado ba ne, a maimakon haka, ya kamata ya kasance abin da zai taimaka wa al’umma wajen daidaita matsalolin da suke fuskanta. Dimokuradiyya mai inganci tana taimakawa wajen gudanar da harkokin kasa da ma raya kasa yadda ya kamata, a maimakon ta zama “misali” ga duniya amma ga tarin matsalolin da ake fuskanta a gida. Baya ga haka, ya kamata dimokuradiyya mai inganci ta taimaka wajen hada kawunan al’umma a maimakon ta haifar da rarrabuwar kawunansu, kuma ta taimaka wajen kiyaye kwanciyar hankalin al’umma a maimakon ta haifar da tashin hankali. Amma idan mun yi nazari a kan da yawa daga cikin matakan da Amurka ta dauka a fagen duniya cikin ‘yan shekarun byaa, za mu gano cewa, tana maganar “dimokuradiyya” ne kawai a fatar baka, amma ba tare da mayar da hankali kan batun bunkasuwar kasa da kasa ba. To, da haka za mu fahimci cewa, tana daukar dimokuradiyya ne a matsayin abin ado kawai, wanda ba zai haifar da alfanu ga al’ummarta da ma kasashe masu tasowa ba.
Amurka dai tamkar wasa take yi wajen gudanar da “taron kolin dimokuradiyya”, don haka ma taron zai zama shirme kawai wanda ba zai haifar da da’a mai ido ba. (Lubabatu)