Tun daga shekarar 2012, shugaban kasar Sin kana babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Mr. Xi Jinping ya sha bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da wanzar da ruhin mazan jiya da suka yi gwagwarmayyar kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
A daidai lokacin da bikin Qingming ke karatowa, wato bikin gargajiya na tunawa da magabata na al’ummar Sinawa, al’ummar Sinawa na tunawa da ‘yan mazan jiya da suka sadaukar da rayukansu, domin kuwa kamar yadda Bahaushe kan ce, “Waiwaye Adon Tafiya”. Duk kabilar da ke da kyakkyawar makoma ba za ta rasa jarumai ba, haka ma abin yake ga kasar da ke da kyakkyawar makoma. Mazan jiya su ne kashin bayan al’ummar Sinawa, wadanda suke ba mu kwarin gwiwar ci gaba. (Lubabatu)