Tsohon shugaban marasa rinjaye majalisr dattawa mai wakiltar mazabar Borno ta kudu Mohammed Ali Ndume, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa neman shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Ndume ya kuma fitar da kudurorinsa 10 da yake son wanzarwa idan ya zama shugaban majalisar.
Ya kuma kasance na farko daga cikin masu neman shugabancin majalisar da ya fara fitar da kudurinsa ga majalisar da kuma ‘yan Nijeriya.
Jaridar LEADERSHIP ta rahoto cewa, Ndume ya taba tsayawa takarar neman shugabanci majalisar ta tara a 2019, amma shugaban majalisar mai ci a yanzu Ahmad Lawan, ya kayar da shi.
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman ‘ya’yan jami’yyarsa da su bar ‘yan majalisar su zabi shugabaninsu da kansu don tabbatar da adalci a ofishin.
Ndume ya bayyana kudirinsa ne a hirarsa da manema labarai a Abuja, inda ya tabbatar da aniyarsa ta neman shugabancin majalisar, inda ya ce, burinsa ya yi dai-dai da matsayin jami’yyar na son yin adalci.