Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugabar hukumar EU, Ursula von der Leyen, jiya Alhamis a birnin Beijing.
Yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin na daukar Tarayyar Turai a matsayin muhimmin karfi a duniya, kuma tana daukar dangantakarsu a matsayin mai matukar muhimmanci a tsarin diflomasiyyarta. A cewarsa, kasar Sin muhimmiyar abokiyar hulda ce ga Turai, wajen shawo kan kalubalen makamashi da hauhawar farashin kayayyaki da inganta takara. Kuma kasar Sin na maraba da EU ta ci gaba da more damarmakin da ci gabanta ya samar.
Shugaba Xi ya kara da cewa, yayin da ake raya hulda tsakaninta da wata kasa, kasar Sin ba ta yin hakan domin wata kasa ta daban, don haka yana fatan EU za ta rike muradunta da muradun dangantakarta da Sin, tare da taka rawar da ta dace wajen raya huldar mai aminci da karko tsakaninta da Sin.
A nata bangare, Madam Von der Leyen ta ce EU bata amince da rarrabuwa ko katse tsarin samar da kayayyaki ba, kuma tana fatan karfafa musaya da tattaunawa tsakaninta da Sin, don kara aiwatar da hadin gwiwa mai amfani. Game da batun Taiwan kuwa, Von der Leyen ta jaddada cewa, EU ba ta da niyyar sauya manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ta amince da gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati daya tilo dake wakiltar dukkan yankunan kasar Sin, kana EU na fatan ganin tabbatuwar zaman lafiya da ci gaba a zirin Taiwan. (Fa’iza Mustapha)