Jiya ne, kamfanoni 36 daga kasashen Sin da Faransa, suka sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 18 a taron majalisar kasuwanci na kasashen Sin da Faransa karo na biyar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya halarci taron a wani bangare na ziyarar kwanaki uku da yake yi a kasar Sin.
A yayin ganawar, wakilan ‘yan kasuwa na kasashen biyu wato Sin da Faransa, sun tattauna don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da samar da wadata da ci gaba ta hanyar hadin gwiwa. Wakilan sun kuma gabatar da shawarwari kan zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Faransa. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp