Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun cafke wani matashi dan shekara 34 dan kasar Amurka dan asalin kasar Suriname mai suna Dadda Lorenzo Harvy Albertb a filin jirgin sama na Fatakwal dake jihar Ribas da laifin shigo da kullin hodar iblis 117 Nijeriya.
Kakakin Hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya bar kasarsa, Suriname, da ke gabar tekun Arewa maso Gabashin Amurka ta Kudu a ranar 2 ga Afrilu zuwa Sao Paulo, Brazil daga kuma Sao Paulo ya sake tasowa zuwa Nijeriya a ranar Juma’a, 7 ga Afrilu, 2023 a jirgin Qatar.
Lorenzo ya bayyana cewa, ya shigo Nijeriya ne yana neman mahaifinsa da ya dade a Nijeriya wanda yake kira da “Omini.”