Kwamishinan ‘yansanda na jihar Filato Mista Batholemew Onyeka ya bayyana cewa, majalisar dokokin jihar za ta cigaba da zama a garkame har sai an samu aminci daga barazanar rashin tsaro a ciki da wajen majalisar.
Onyeka ya bayyana wa manema labarai hakan a yau Talata a garin Jos kan dalilan da suka sa jami’an tsaro suka garkame majalisar a ranar 5 ga watan Afrilun 2023.
Ya bayyana cewa, rundunar ‘yansandan jihar ta samu rahoton sirri kan wani hari da ake shirin kaiwa majalisar, inda harin zai iya janyo karya doka da oda.
Onyeka ya kara da cewa, rundunar ta hanyar kafar sada zumunta ta tattaro bayanan cewa, tsohon shugaban majalisar Abok Ayuba wanda aka tsige a ranar 28 ga watan Oktobar 2021, ya samu nasara a kotu na cewa, a sake dawo dashi kan kujerarsa.
Acikin rahoton sirri, rundunar ta samu bayanan cewa, wasu marasa kishin kasa masu son zuciya na kokarin tada tarzoma a majalisar.
A cewarsa, bisa samun wannan bayanan na sirrin, “mun gayyaci ‘yan majalisar tare da lauyoyinsu zuwa ofishinna, inda aka shawarcesu da su gujewa yin duk wani abun da zai janyo karya doka da oda.”