Ana sa ran Sadio Mane zai ba da hakuri a gaban ‘yan wasan Bayern Munich bayan ya naushe abokin wasansa Leroy Sane a fuska bayan da Manchester City ta doke su a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Talata.
Jaridar Sky Germany ta ruwaito cewa leben Sane ya zubar da jini bayan rikicin da ya kaure a tsakanin ‘yan wasan a dakin hutu wanda har sai da sauran abokan wasansu suka shiga tsakani don raba su.
Mahukunta kungiyar ta Bayern Munich sun gudanar da wani taron gaggawa a ranar Laraba don tattauna yiwuwar hukunta Mane.
Ana sa ran Mane zai ba da hakuri a gaban ‘yan wasan kungiyar yayin atisayenta na ranar Alhamis.
Manchester City mai masaukin baki ta lallasa kungiyar Bayern Munich a filin wasa na ettihad da ci 3:0.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp