Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya amince a biya ma’aikatan jihar albashin watan Afrilun 2023 don gudanar da bikin sallah karama cikin nishadi.
Hakan na kunshe ni a cikin wata sanarwa da tawagar yada labarai ta gwamnan ta fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce, tun bayan rantsar da gwamnantin acikin shekaru hudu da suka gabata, gwamna Zulum ke gudanar da irin wannan matakin, musamman domin ma’aikatansa su samu damar gudanar da shirye-shiryen shagulgulan bikin Ibada cikin nishadi.
Sanarwar ta tabbatar da cewa, tuni ma’aikatan suka fara ganin albashinsu na shiga cikin Asusun ajiyarsu na bankuna.
Sanarwar ta bayyana cewa, Zulum ya sha shelanta cewa, biyan albashin ma’aikatan gwamnatin jihar, ba sa daga cikin ayyukan ci gaba na gwamnatinsa domin biyan albashin tamkar biyan bashi ne na aikin da ma’aikata suka yi kuma bai taba yin wasa da biyan albashi da kudin ‘yan fansho ba.
Sanarwe ta ce, gwamnan ya kuma amince da a fitar da sama da Naira biliyan 20 domin a biya garatutin ma’aikatan gwamnatin jihar da suka yi ritaya.
A cewar sanarwar, gwamnatin jihar akasari ta na biyan albashin ma’aikatan ta ne daga ranar 25 zuwa ranar 26 na ko wanne wata, amma idan wani bikin Ibada – Sallah ko Kirsimeti ya taso, Zulum na biyan albashin ma’aikatan ne daga ranar 15 zuwa 17.