Kasar Sin ta yi kira ga kungiyar G7 da ta daina karkatar da hankalin al’umma ko kuma neman haifar da fito-na-fito. Kasar Sin ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga sanarwar taron ministocin harkokin wajen kungiyar G7 da ta shafawa kasar bakin fenti.
Yayin taron manema labarai na yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, kungiyar G7 ta yi biris da matsayin kasar Sin tare da yin watsi da hujjoji, kana ta yi katsalandan cikin harkokin gidan Sin da kuma bata mata suna. Ya ce kasar Sin na bayyana rashin gamsuwarta da kakkausar murya kuma ta na adawa da hakan, sannan ta mika korafinta ga kasar Japan.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar da safiyar yau bayan kammala taronsu a Japan, ministocin na kungiyar G7 sun jaddada abun da suka fada wato muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan tare da ikirarin sun damu da yanayi a yankin tekunan gabashi da kudancin kasar Sin da jihar Xinjiang da kuma Tibet.
Baya ga haka, taron ya zuzuta bazaranar nukiliyar kasar Sin, inda Wang Wenbin ya ce kungiyar G7 ta yi watsi da hujjoji, kuma tana yunkurin karkatar da hankalin jama’a, yana mai cewa kungiyar ba ta wakiltar daukacin al’ummun kasa da kasa. (Fa’iza)