Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dinga girmama junansu.
Ya sanar da hakan ne a sakonsana sallah ga Musulman kasar nan bayan kammala Azumin Ramadan.
- Yadda Ake Zakkar Shan Ruwa Da Sallar Idi
- Bikin Sallah: Dauda Lawal Ya Taya Musulmi Murna, Ya Nemi A Dage Da Addu’a
A cewarsa, zaben 2003 da da aka kammala cikin nasara, na daga cikin nasarar da gwamnatinsa ta samu, musamman kin yin katsa-landan da gwamnatinsa ba ta yi a cikin zabukan.
Ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar, inda ya ce sakamakon sahihin zaben da aka gudanar na daga cikin tarihin da gwamnatinsa ta bari a kasar nan.
Ya kuma taya Musluman kasar nan murnar kammala Azumin watan Ramadan a cikin nasara, inda ya yi addu’ar Allah ya biya su sadaukarwar da suka yi.
Shi ma a na sa sakon na Sallah, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, kira ya yi ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa shugabannin kasar nan addu’oin zaman lafiya da kawo karshen rashin tsaro da mika gwamnati ga sabuwar gwamnati mai zuwa cikin nasara.
Shi kuwa shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a cikin nasa sakon da hadiminsa na yada labarai, Lanre Lasisi ya fitar ya taya Musulami murnar kammala Azumin watan Ramadan cikin nasara, inda ya bukace su da su ci gaba da aiwatar da darusan da suka koya a cikin watan.
Haka zalika, mataimakin shugaban majalisar wakilai Ahmed Idris Wase, kira ya yi ga Musumi da su da su yi koyi da darusan da suka koya a cikin watan Ramadan.
Bugu da kari, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a nasa sakon na Sallah ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin cewa ba zai gaza ba bayan ya karbi shugabancin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu.
Tinubu ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya sanya wa hannu, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da kaunar junansu.
Shi ma dan takarar shugaban kasa na jami’yyar PDP, Atiku Abubakar a nasa sakon na Sallah ya cewa ya yi akwai bukatar ‘yan Nijeriya da su rungumi zaman lafiya da gujewa raba kan kasa.