Bisa gayyatar da aka yi masa, da yammacin yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky. Yayin zantawar ta su, shugabannin biyu, sun yi musayar ra’ayoyi game da alakar kasashen biyu da batun rikicin Ukraine.
A nasa tsokaci, Xi Jinping ya bayyana cewa, duk irin sauyin da aka samu a harkokin kasa da kasa, Sin a shirye take ta yi aiki tare da Ukraine, wajen ingiza hadin gwiwar cimma moriyar juna tsakanin kasashen 2.
Game da rikicin Ukraine kuwa, shugaba Xi ya ce kasar sa za ta ci gaba da goyon bayan wanzar da zaman lafiya, kuma muhimmin burin ta zai kasance bunkasa zaman lafiya, da ingiza komawa shawarwari.
Ya ce yana fatan dukkanin sassan da batun ya shafa za su yi nazari mai zurfi game da rikicin Ukraine, su kuma yi aiki tare ta hanyar tattaunawa, ta yadda za a kai ga hawa turbar wanzar da zaman lafiya, da daidaito na tsawon lokaci a yankunan Turai.
Bugu da kari, shugaban na Sin ya ce gwamnatin sa za ta aike da wakilin musamman game da batutuwan Turai da Asiya, domin ya ziyarci Ukraine, da sauran wasu kasashem yankin, ta yadda za a kai ga zurfafa zantawa da dukkanin sassa, game da matakan shawo kan rikicin Ukraine ta hanyar siyasa.
Kaza lika, Sin za ta samar da rukunonin tallafin jin kai ga Ukraine, kuma a shirye take da ta ci gaba da ba da duk wani taimako ga kasar gwargwadon karfin ta.
A nasa bangare kuwa, shugaba Zelensky, ya ce Sin na nacewa ka’idoji da dokokin MDD, a fannin harkokin kasa da kasa, tana kuma taka rawar gani a harkokin kasa da kasa. Ya ce Ukraine na godiya bisa tallafin jin kai da Sin din ke samar mata, tana kuma maraba da muhimmiyar rawa da Sin din ke takawa bangaren dawo da zaman lafiya, da warware rikicin kasar ta hanyar diflomasiyya. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)