Shugaba Buhari a yayin zaman majalisar Zartarwa ta tarayya da ake gudanar a duk ranar Laraba a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya rantsar da sabbin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya shida.
Wadanda aka rantsar sune, Adam Mahmud Kambari, jihar Borno; Esuabana Nko Asanye, jihar Kuros Ribas; Lamuwa Adamu Ibrahim, jihar Gombe; Yakubu Adam Kofar-Mata, jihar Kano; Oloruntola Olufemi Micheal, jihar Ogun sai Richard Pheelangwah daga jihar Taraba.
Daga cikin mahalarta zaman majalisar sun hada da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Shugabar ma’aikata, Dakta Folasade Yemi-Esan da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.
Daga cikin ministocin da suka halarci zaman majalisar akwai miniatar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed; ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed da kuma ministan Abuja Mohammed Musa Bello.
Sauran sune, Otunba Niyi Adebayo ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Farfesa Ali Pantami ministan sadarwa da bunksa tattalin arziki na zamani, Abubakar Aliyu ministan karafa sai kuma ministan kwadago da ayyuka, Dakta Chris Ngige.
A hirarta da manema labarai na fadar shugaban kasa, Folashade Yemi-Esan, ta yi kira da sabbin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya da aka nada da su yi aiki tukuru don bayar da ta su gudunmawar a kasar nan.