Jiya Talata 25 ga watan nan na Afirilu, rana ce ta dakilewa, da kuma kandagarkin cutar zazzabin cizon sauro ta duniya. A ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2021 ne hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta sanar da karewar cutar a kasar Sin.
A jiya Talata, a yayin biki mai nasaba da hakan da aka shirya a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, wani jami’in hukumar dakilewa, da kandagarkin cututtuka ta kasar Sin CDC, ya bayyana cewa, kawar da cutar a kasar Sin, wani sabon mafari ne.
Kuma kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da cutar ba ta sake bulla ba, da yaki, da kuma kaucewa shigar ta Sin daga ketare, tare da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa, da taimakawa kasashen duniya wajen yaki da cutar, a kokarin raya duniya maras wannan cuta.
Shi ma a nasa tsokaci yayin taron, shugaban cibiyar dakilewa da kandagarkin cututtukan da ake kamuwa da su sakamakon cudanya da kwari, karkashin hukumar ta CDC Zhou Xiaonong, ya ce kyawawan matakan da kasar Sin ta dauka wajen samun nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro a gida, suna amfanar kasashe da yankunan dake fama da yaduwar cutar.
Ya ce sakamakon kokarin da kasar Sin take yi a cikin dogon lokaci, ya sa kayayyakinta, da hanyoyinta masu nasaba da wannan aiki sun samu amincewa daga WHO, da raguwar kasashen duniya.
Zhou ya kara da cewa, nan gaba kasar Sin za ta amsa kiran gina al’ummomin kasa da kasa mai makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya, kana za ta kara taimakawa kasashe masu tasowa, wajen kawar da cutar baki daya. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp