Jiya Talata 25 ga watan nan ne kwamitin sulhu na MDD, ya yi tattaunawar gaggawa game da halin da ake ciki a kasar Sudan. Yayin zaman, wakilin kasar Sin ya yi kira ga bangarori 2, masu ruwa da tsaki a rikicin kasar ta Sudan, da su hanzarta tsagaita bude wuta a tsakaninsu, tare da bukatar kasashen duniya da su girmama ikon mulkin kan Sudan, da ba ta damar ba da jagoranci, da sauraren ra’ayoyin Sudan da kasashen da ke yankin ta.
A nasa bangare kuwa, babban magatakardan MDD António Guterres, ya sake jaddada cewa, tilas ne a gaggauta dasa aya ga wannan rikici. Ya kuma yi kira da a tsagaita bude wuta nan take, tare da bukatar kasashe mambobin kwamitin sulhu, da kasashen da ke yankin, su matsa wa bangarorin 2 na Sudan lamba, a kokarin sassauta zaman dardar a kasar.
Shi ma zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, cewa ya yi a matsayinta na abokiya, kuma aminiyar Sudan, kasar Sin ta yi bakin ciki game da sake barkewar fada a Sudan. Tana kuma kira ga bangarori 2 na Sudan, da su mayar da muradun kasa, da na jama’a a gaban komai, su tsagaita bude wuta cikin sauri, a kokarin kaucewa tabarbarewar halin da ake ciki a kasar.
Zhang Jun ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na goyon bayan ikon mulkin kan Sudan, da ’yancin mulkin cikakkun yankunanta, kana tana fatan ganin kura ta kwanta a Sudan cikin hanzari, ta yadda kasar za ta sake samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali, ta kuma koma kan hanyar da ta dace ta raya kanta.
Kafofin yada labaru na Sudan sun ruwaito cewa, a daren jiya Talata, ma’aikatar lafiyar Sudan ta ce, mutane 460 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 4,063 suka jikkata, sakamakon dauki ba dadin da dakarun Sudan, da rundunar RSF suka gwabza a sassan jihohi kasar 11. (Tasallah Yuan)