Zababben Gwamnan Jihar Adamawaz Ahmadu Fintiri, ya bukaci rundunar ‘yansanda ta kasa da ta, hukunta wadanda suke da hannun wajen taka dokar zabe wajen ayyana ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar.
Bukatar ta gwamnan na kunshe ne cikin wasikar da ya turawa rundunar, inda ya nemi rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Hakimi A Zamfara
- Kasar Sin Ta Tura Jirgin Ruwan Soja Don Kwashe Jama’ar Ta Dake Sudan
Idan ba a manta ba, ana kan tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa ne, sai kwamishinan hukumar zaben jihar, Hudu Yunusa-Ari ya bayyana Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben inda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta shiga tsaka don dakatar da haramtaccen zaben.
Atoni-Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Afraimu Jingi ya rattaba hannu kan wasikar.
Gwamnatin jihar ta kuma sha alwashin bayar da goyon bayan don ganin an kai karshen binciken, inda kuma gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda matakin na Yunusa-Ari, ya janyo babbar barazana ga zaman lafiyar jihar da gwamnatin jihar ta shafe shekaru hudu da tabbatarwa.