Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Buhari kana suka yi sallar Juma’a tare a masallacin fadar shugaban kasa da ke Aso Rock Villa, Abuja.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda yace kafin su shiga Sallar Juma’a, sun yi ganawar sirri, inda suka gaisa da juna kuma suka taya juna murnar kammala azumin Ramadan da murnar bikin Sallah.
Zababben shugaban kasar ya samu rakiyar kakakin majalisar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila da gwamnoni biyu, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na Kano da Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara da kuma Alhassan Ado Doguwa shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp