A yau Asabar ne kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin, ya ba da kididdigar cewa, yawan fasinjojin da za a yi jigilar su a ranar farko ta hutun ranar ‘yan kwadago zai kai mutum miliyan 19.5, adadin da ya kai matsayin koli a wata rana guda. Hukumomi masu ruwa da tsaki na kokarin habaka karfinsu don tabbatar da ingancin ayyukan sufuri, kuma yawan jiragen kasa da za a amfani da su yayin wannan aiki zai kai 11,873.
A cewar kamfanin, a jiya Juma’a, yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ya kai miliyan 15.45, kuma jiragen kasa suna zirga-zirga yadda ya kamata. Daga cikinsu, sashin birnin Beijing ya yi jigilar fasinjoji miliyan 1.33, yayin da adadin a Shanghai ya kai fiye da miliyan 3, sai kuma birnin Guangzhou mai adadin da ya kai miliyan 2.2.
A yau Asabar, adadin a birnin Beijing zai kai miliyan 1.53, a Shanghai kuma, zai kai miliyan 3.7, sai birnin Guangzhou da zai kai miliyan 2.96, kuma duk wadannan alkaluma sun kai matsayin koli a tarihi a tsakanin daidaikun ranaiku. (Amina Xu)