Gwamnan jihar Edo Goodwin Obaseki ya ce gwamnatinsa za ta kashe Naira biliyan 6 wajen sake inganta gine-ginen makarantun sakandare a jihar a tsakanin watan Mayu zuwa Satumba na shekara mai zuwa.
Ya ce rashin adalci ne a yi tsammanin gwamnatinsa a shekaru biyar ko takwas za ta magance matsalar makarantun jihar da ta taru sama da shekaru 60.
Obaseki wanda ya bayyana hakan a karshen mako a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan kammala taron bikin makarantun Edo na 2023, ya ce yana son ya bar tsari mai kyau kan abubuwan da ya kamata a yi da kuma lokacin da za a yi a cikin tsarin makarantun.
“Tsakanin ranar 1 ga watan Mayu zuwa Satumba na shekara mai zuwa, duk kudin da na yi amfani da su wajen gudanar da aikin titin Seefor a yanzu zai tafi kan makarantun sakandare kuma wannan ya haura Naira biliyan 6 kan makarantar sakandire kadai.
“Muna da Hukumar Ilimi ta bai daya (UBEC) ta tarayya da ke tallafa wa Hukumar Ilimi ta jiha (SUBEB) amma ga Makarantun Sakandare, babu wani tallafi, don haka dole ne mu samar da tsarin sake gina dukkan makarantunmu na Sakandare. Amma ba za mu iya kammala dukkan makarantun ba amma mun fara da tsarin samar da kudade.” inji shi