- A Yi Adalci Kowa Ya Samu Hakkinsa
- Masu Koken Banza A Nuna Musu Kuskurensu
- Wanda Ya Ci Zabe Ya YI Hamdala, Haka Wanda Ya Fadi
- Babu Wata Ka’idar Da Ta Ba Da Damar Tashin Hankali
- ‘Yan Siyasa Mun San Amfanin Zaman Lafiya
Daga lokacin da aka sanar da wadanda suka lashe zabukan da aka gudanar na shekarar 2023 a Nijeriya, manyan kasa da sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da bayyana alkiblar da ta kamata sabbin shugabannin da za a rantsar su fuskanta domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa da ake fatan gani a Nijeriya.
Za a iya cewa, a wannan karon, yadda mutane suke kokarin haska hanyoyin da ya kamata shugabannin su bi, ba zai rasa nasaba da irin ce-ce-ku-ce da sabon salon da zabukan 2023 suka zo da su ba ta fuskar kabilanci, bangaranci da kuma uwa-uba batun addini wanda ya fito fili baro-baro saboda tikitin takarar musulmi da musulmi da jam’iyya mai mulki ta bai wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashin Shettima.
Da yawa kafin zaben na 2023, an yi hasashen takarar shugaba da mataimakinsa mabiya addini daya ba zai yiwu ba a Nijeriya a halin yanzu, duk da cewa an yi hakan a zaben da aka yi na Abiola da Kingibe a 1993 wanda ba a ayyana sakamakonsa ba a hukumance. Saboda ana ganin akwai wutar kiyayya da ke ruruwa da aka cinna ta bangaren bambancin addini da kabilanci fiye da kowane lokaci da ya shude a Nijeriya.
Har ila yau, bayan ayyana sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, jam’iyyun adawa musamman manyansu, PDP wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da mataimakinsa Gwamna Okowa na Jihar Delta suka yi wa takara da kuma LP wacce Peter Obi da mataimakinsa Datti Baba-Ahmed suka rike kambinta a zaben, sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana. An saba da fatali da sakamakon zabe daga jam’iyyun adawa a kowane zabe kuma a duk duniya ba Nijeriya ba kadai, amma zanga-zangar da Atiku ya jagoranta da kansa tare da kusoshin jam’iyyarsa a Abuja, ta nuna irin matukar adawa da ayyana Tinubu da Kashim a matsayin wadanda suka yi nasara.
Haka nan ikirarin da Peter Obi ya yi na cewa shi ne ya lashe zaben ba Tinubu ba, da kiran da mataimakinsa Datti Baba-Ahmed ya yi na cewa kar a rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban kasa a ranar 29 ga Mayun 2023 da kuma kiraye-kirayen da wasu magoya bayansu ke yi na cewa ko a bai wa su Obi nasarar lashe zabe ko kuma a raba Nijeriya, sun kara tunzura musamman ‘yan jam’iyyar APC da suke ganin nema ake a yi musu ta-leko-ta-koma.
Wakazalika, yadda sakamakon zabukan na 2023 suka yi ba-zata a wasu wurare, wadanda ake ganin za su lashe suka zama sun sha kaye saboda rawar ganin da bambancin addini ya yi, da wata hira ta wayar salula da aka yi zargin Peter Obi ya yi da Shugaban Cocin Libing Faith Church Worldwide, Bishop Dabid Oyedepo a kan cewa zaben tamkar wani yaki ne na addini, wata alama ce da ke nuna cewa akwai babban kalubale a gaban shugabannin da aka zaba musamman wajen cire wa ‘Yan Nijeriya kiyayyar juna saboda bambancin addini da kabila da bangare.
A kan haka, wakilinmu na fadar shugaban kasa, Jonathan Nda-Isaiah, ya yi wata ‘yar kwarya’kwaryar tattaunawa da shugaban majalisar dattijai ta kasa, Sanata Ahmed Lawan game da kalubalen da ke gaban shugabannin da aka zaba da za su karbi ragamar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023.
Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa lallai akwai bukatar sabbin shugabannin su zage damtse wajen hada kan ‘Yan Nijeriya, domin kamar yadda ya bayyana, “Haduwar kan ‘Yan Nijeriya ai aikin shuwagabannin Nijeriya ne. Mutanen da aka zaba su kasance shuwagabanni suna da aikin kawo ‘Yan Nijeriya su tabbatar cewa an yi adalci a kowane lokaci. Kuma a tabbatar cewa ba a nuna wariya saboda bambancin addini ko kuma inda mutum ya fito ba.”
A cewarsa, duk yadda shugabannin da aka zaba suka so aiwatar da ayyuka na ci gaba, ba za su samu nasarar da suke so ba sai an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, yana mai cewar, “Tun da mu ‘yan siyasa ne, mun san amfanin a zauna lafiya, mun san amfanin hadin kai. Duk inda aka ce ba a samu hadin kai ba, ba a samu zaman lafiya ba, ba yadda za ka samu ci gaba. Saboda haka, wannan ya ta’allaka ne a kansu ko kuma mu shuwagabanni da aka zaba.
“Kuma ina so in tabbatar wa jama’a cewa, daga shi shugaban kasan da aka zaba, Sanata Bola Ahmed Tinubu Asiwaju da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima da sauranmu da aka zaba a matsayin ‘yan majalisa da sauran wadanda za a sa a matsayin ministoci da sauran manya-manyan ma’aikata da za a sa a gaba, kowane daya daga cikinmu zai tabbatar ya yi abin da ya dace saboda a samu hadin kai a kasar nan ba a wargaza kan mutanen kasar ba.” In ji shi.
Bugu da kari, Sanata Ahmed Lawan ya yi kira ga wadanda alhaki ya rataya a wuyansu a kan cewa duk wanda ya kawo koke a kan wani abu da aka yi masa ba daidai ba, a saurare shi a yi masa adalci, sannan idan koke ne na banza to a nuna masa kuskurensa.
“Kuma yayin da wani yake jin cewa shi ba a yi masa daidai ba, ya kamata a saurara, in na gaske ne a kan cewa akwai matsala ba a yi daidai din ba to a gyara, in kuma kuka ne na banza to a nuna wa mutumin nan ko kuma mutanen nan cewa kukan banza suke yi, ba daidai ba ne. Ya kamata dai a yi adalci a tabbatar kowa ya samu hakkinsa.” Ya bayyana.
Da aka tambaye shi game da masu yi wa Nijeriya barazana, ya amsa da cewa, “ban san me kake nufi da masu yi wa Nijeriya barazana ba?”, da aka ce masa ana nufin ‘yan siyasa masu cewa ko a yi su ko kuma duk yadda kasar za ta yi ma, ta yi. Sanata Ahmed Lawan ya amsa da cewa, “To, ni ban san su ba. Amma dai duk dan siyasar da zai shiga zabe to ai ba mai yi wa kasa barazana ba ne. Ka san dama ko ka ci ko ka fadi ne. In ka ci ka yi hamdala, in ka fadi ma ka yi hamdala. Amma in ka fadi ka ce za ka yi bore, za ka yaga kasa, za ka yi tashin hankali, to ka san cewa akwai hukuma. Kuma hukuma kamata ya yi duk wanda ya tada hankali ba bisa wani ka’ida ba, ba ma ka’idar da za ka samu na tada hankali, to hukuma ta yi maganin mutum.
“Babu wani abu daban, in ka ci zabe, ka ci zabe, in kuma ka fadi zabe to ko ka je kotu ka nemi a fayyace cewa kai ka ci ba wanda aka ce su ne suka ci ba, ko kuma ka tabbatar cewa ka fara shirinka na wasu shekara hudu a gaba. Amma ba daidai ba ne mutum ya yi tunanin cewa in bai ci zabe ba shikenan kasar nan sai dai a ruguza ta, to hukumomi me suke yi? Duk wanda ya ce za a ruguza kawai saboda son zuciyarsa to hukumomi su yi maganin sa.” A ta bakin Sanata Ahmed Lawan.
Yanzu haka dai hankula sun karkata a kan shirye-shiryen mika mulki a karshen wannan watan, inda kuma ake ci gaba da gwagwarmayar neman shugabancin majalisun dokoki na kasa a bangaren dattawa da na wakilai. Ba a dai san maci-tuwo ba sai miya ta kare saboda yadda ake rububin kujerun shugabancin, da irin siyasar cikin gidan da ake bugawa a APC mai kujeru mafi rinjaye a majalisun.