Masu garkuwa da mutane sun sace ‘ya’yan mai martaba Sarkin Kagarko da ke jihar Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar tare da wasu jikokinsa.
Wadanda aka sace din, mafi yawancinsu yara ne, kuma har yanzu ba a san inda masu garkuwar suka kaisu ba.
An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a makon da ya gabata a cikin dare.
Sai dai, har yanzu mahukuntan ‘yansanda a jihar, ba su fitar da wata sanarwar kan afkuwar lamarin ba.
Amma wani shugaban matasa a karamar hukumar ta Kagarko Adamu Abubakar ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa, da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadin da ta gabata ne, masu garkuwar suka kai harin a fadar Sarkin, inda suka wuce sashen kwanan ‘ya’yan Sarkin kai tsaye suka sace ‘ya’yan Sarkin tara da kuma wasu jikokinsa wadanda mafi yawancinsu kananan yara ne.
A cewarsa, masu garkuwar sun kuma yi awon gaba da daya daga cikin matan Sarkin, inda daga baya, ta samu nasarar arce wa daga gun masu garkuwar.
Ya ce, har yanzu ba a san inda masu garkuwar suka kai yaran ba.