Rahotonni daga kasar Pakistan sun bayyana cewa, ‘Yansandan kasar sun kama tsohon Firaministan kasar, Imran Khan a gaban wata babbar kotu da ke babban birnin kasar a Islamabad.
An gabatar da kararraki goma sha biyu kan dan siyasar mai shekaru 70 tun bayan hambarar da shi daga mulki. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun yi kokarin tsare shi a lokutan baya amma magoya bayansa suka hana jami’an.
A shekarar da ta gabata, ya tsallake rijiya da baya a harin da aka kai wa ayarin motocinsa a lokacin da yake shugabantar wata zanga-zangar adawa da gwamnati.
Kamen Khan na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin kasar suka zarge shi da yin wasu zarge-zarge marasa tushe a kan wani babban jami’in hukumar leken asiri, Inter-Services Intelligence (ISI).
Tsohon Firaministan a wani bidiyo da ya fitar ta shafin kamfanin sadarwa na Tehreek-e-Inset (PTI) a manhajar YouTube ya nanata cewa an tsare shi ne bisa zarge-zargen karya da sam bai san da su ba kuma wannan shirin mulkin kama karya ne sabuwar gwamnatin ke shirin yi.