Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana yau Talata cewa, karuwar cinikin waje na kasar a cikin watanni hudu na farkon shekarar bana ta kai kaso 5.8 bisa dari, kan na makamancin lokaci na bara, wato cinikin wajen kasar yana ci gaba da karuwa yadda ya kamata.
Alkaluman kididdigar hukumar sun nuna cewa, a cikin watanni hudu da suka gabata, darajar adadin karuwar cinikin waje na kasar ya kai kudin Sin yuan triliyan 13.32, adadin da ya karu da kaso 5.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Kaza lika daga cikin adadin, darajar kayayyakin da ake fitarwa zuwa ketare ya kai yuan triliyan 7.67, adadin da ya karu da kaso 10.6 bisa dari, kan na makamancin lokaci na bara, kana adadin darajar kayayyakin da aka shigo da su daga ketare ya kai yuan triliyan 5.65, adadin da ya karu da kaso 0.02 bisa dari.
Kaza lika, darajar adadin cinikin dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, ya kai yuan triliyan 4.61 a cikin watanni hudu na farkon bana. (Mai fassarawa: Jamila)