Hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya da ke kasar waje (NIDCOM) ta bayyana cewa, rukuni na 11 da ya tattaro mutum 128, 117 da suka taso daga filin jirgin sama na kasar Sudan, zasu sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 9 na safiyar gobe Alhamis.
Hukumar ta ce, za su iso Nijeriya ne a cikin Jirgin sama na Tarco Air, inda NIDCOM ta bayyana cewa, babu rai daya da aka rasa daga cikin wadanda aka kwaso, inda jimillar ‘yan Nijeriya su kai kai 1,984 da aka kwaso ya zuwa yanzun.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, aikin hadaka da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA da ma’aikatar bayar da agajin kan afkuwar annoba ta kasa, NIDCOM da kuma hukumar gwamnatin tarayya da ke kula da masu gudun hijira, sun bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kwaso ‘yan Nijeriya daga Sudan.
Har ila yau, hukumar zana jarrabawa JAMB, ta yi alkawarin bayar da dukkan goyon bayan da ya dace don tabbatar da daliban da aka kwaso sun samu guraben karatu a jami’oin cikin gida Nijeriya.