Gwamnatin jihar Kano mai jiran gado karkashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf ta bayyana aniyarta na kwato kadarorin al’umma da ake zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sayar wa ‘yan’uwansa.
A cewar Dr. Abdullahi Baffa Bichi, shugaban kwamitin amso kadarorin gwamnati na jam’iyyar NNPP mai shirin karbar mulki, tace an sayar da ofishin hukumar da ke kula da bin doka da ke kan titin State Road a kan kudi kalilan – naira miliyan 10 ga Abba Ganduje, amma yanzu an kimanta kudin ginin akan kudi sama da Naira miliyan 300.
A wata sanarwa da Dr. Bichi ya raba wa manema labarai a Kano, ya nuna matukar damuwarsa game da abin da gwnatin mai barin gado ta yi, wanda ya bayyana a matsayin barnatar da dukiyoyin jama’a.
Ya kara da cewa gwamnati mai jiran gado za ta nemo duk wata hanya ta doka da ta dace don kwato kadarorin jama’a da ake zargin an sayar da su.