Mahaifiyar shugaban kasar Sin Xi Jinping, Qi Xin ta kan rubuta masa wasika bayan ya zama shugaban kasar Sin, don karfafa masa gwiwar sadaukar da ransa wajen biyan bukatun jama’a, da tunatar da shi kada ya manta nauyin dake wuyansa da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata. Fatan mahaifiyarsa ya zama tushen ruhinsa na gudanar da ayyukansa na siyasa.
A watan Disamban shekarar 2016, a karon farko, Xi Jinping ya gana da wakilan iyalai mafi da’a a kasar, inda ya jaddada cewa, dole ne a koyawa kananan yara nagartattun ra’ayi da dabi’u da da’a, don su zama mutanen kwarai dake iya bautawa kasa da jama’a.
A bikin murnar sabuwar shekara ta 2017, Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taba zuciya, inda ya ce kada a manta da iyalai duk da tazara mai tsawo dake akwai, da ma dimbin ayyukan da ake da su.
Kauna daga mahaifiya ta taimakawa yara gadon nagartattun dabi’a da da’a, kuma wadannan kyawawan halayya, za su amfanawa al’umma. Ci gaban ko wanne gida yana ingiza bunkasuwar wata kasa, gudunmawar da duk wani iyali ya bayar, zai hadu waje guda don zama karfi mai inganci na farfadowar al’ummar Sinawa baki daya. (Amina Xu).