Da yammacin yau Litinin, agogon Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Eritrea, Isaias Afwerki dake ziyara a kasar, a babban dakin taron jama’a.
Yayin ganawar, Xi Jinping ya bayyana cewa, ba tare da la’akari da yadda yanayin duniya zai kasance a nan gaba ba, mutunta juna da fahimta da goyon baya da taimako, su ne har kullum za su kasance tubalin abota tsakanin Sin da kasashen Afrika.
A cewarsa, a shirye Sin take ta hada hannu da nahiyar Afrika wajen inganta daddadiyar abotarsu da karfafa aminci da juna da samar da sabbin damarmaki ga Afrika daga ci gaban kasar da ma tafarkinta na zamanantar da kanta da kuma inganta gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya.
A nasa bangare, Isaias Afwerki, ya bayyana cewa, yanayin da duniya ke ciki a yanzu yana kan wata muhimmiyar gaba, kuma har yanzu kasashen Afrika na fuskantar babakere da wasu dabi’un na rashin adalci.
Ya ce kasashen duniya na fata tare da imanin cewa, kasar Sin za ta bayar da karin gudunmuwa ga inganta rayuwar bil adama da samar da ci gaba da kuma tabbatar da adalci tsakanin kasa da kasa. (Mai fassarawa: Mustapha Fa’iza)