Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma ta fanni da dama. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da dabi’ar wasu mazan ta yin waya da ‘yan matansu na waje a gaban matansu na aure, wanda kuma ba suda wata alaka ta aure (Kai kudi ko saka rana) tsakaninsu da ‘yan matan. Yin hakan ga masu dabi’ar ba komai bane a wajensu, inda sabo an saba dabi’arsu ce a haka, dan wani in matar ta tambaye shi dalilin yin hakan, ba shi da wata amsa face cewa dabi’ar sa ce hakan, ko dan ya shirya rabuwa da ita ne kuma oho! Kamar dai yadda ya faru a kan wata baiwar Allah.
Da yawan Mata na kokawa game da irin wannan matsalar, wanda rayuwarsu takan zama abar tausayi, musamman lokacin da mazajen nasu suka fara yunkurin bayyana musu asalin dabi’arsu ta hira da ‘yan mata a gabansu ba tare da shakku ko tsoron komai ba, a ganinsu yin hakan tamkar sun zama wasu Jarumai ne cikin maza marasa tsoro. Sai dai kuma a duk lokacin da namiji me irin wannn dabi’ar ya je neman auren macen ba zai taba bayyana mummunan dabi’arsa ba, sai dai ya aro dabi’ar wasu ya saka wato kyakkyawar dabi’a sa’annan ya je, zai bar dabi’ar ne har sai bayan an yi aure, zuwa lokacin daya daukarwa kansa maida dabi’arsa ta asali.
Wani namijin ya kan dauki lokaci kamar shekara guda kafin ya dawo da asalin dabi’arsa, yayin da wani kuma ko shekarar ma ba zai bari tayi ba, domin baya bukatar samun karuwa tsakaninsu tunda ya san yadda asalinsa ya ke na ‘auri saki’, daga nan ne kuma zai fara fito da dabi’unsa filla-filla dan kawai ta tanka ya tura ta waje ya samo wata. Ko da ace mace na hakuri da irin dabi’arsa yau da gobe sai Allah, hakan ke sa wasu matan kasa jurewa har ta kai ga sun tanka, wanda a karshe saki ya biyo baya ba tare da sun shirya afkuwar hakan ba, Namiji zai saki Mace ko da kuwa da jariri tsakaninsu.
Abin takaicin shi ne; hakan ya fi afkuwa ga matan da suka taba yin aure (Zawarawa), maza masu irin wannan dabi’ar sukan aure su matsayin mata ta biyu ko akasin haka, wanda ko da ace Namiji yana da wata matar ba zai aikata hakan a gaban uwargidan ba, sai dai ya aikata akan matar daya auro ko dan a lakana mata cewar ‘Taki Zaman Aure’. Sai dai akan rasa gane inda maza masu irin wannan dabi’a suka dosa a duk lokacin da suka aikata hakan. Mabiya shafin Taskira sun bayyana nasu ra’ayoyin game da wannan batu kamar haka:
Sunana Abba Abubakar daga Jihar Jos:
Wannan darasi ne mai muhimmanci, da ya dade yana haifar da damuwa ga al’amarin zamantakewar aure. Ni dai duk da ina namiji ban yarda da irin wannan halayyar ta nuna ko -in-kula da mutunci da kimar matar mutum. Bai dace namijin da ya san abin da yake yi, ya dauki waya ya kira wata wacce ba matarsa ba, ko ya yi hira da ita a gaban matarsa ta Sunnah ba. Aure ba abin wasa ba ne, ko da wasu mazan na ganin suna da ‘yancin su kara aure ko su nemi wasu matan, wanda ita matar ba ta da wannan damar. Amma zamanta matarsa ya ba ta kariya da wata kima da bai kamata a zubar mata da shi ba. An sani mata suna da tsananin kishi, a kan abin da suke so, bai dace a yi wasa da wannan abin da suke ji a ransu ba. Domin sai mace na sonka ne ma za ta nuna maka kishinta. Shawarata ga matar da ta yi yaji ko ta bar dakin mijinta saboda nuna rashin jin dadinta ga halayyarsa, ta yi hakuri ta koma ta zauna a dakin mijinta. A hankali sai ta ci gaba da yi masa nasiha da addu’a, har ya gane rashin dacewar abin da ya ke yi. Kuma idan yana waya a kusa da ita, ta tashi ta bar wajen, ta je ta yi wani abin da zai amfane ta.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
A gaskiya wannan hali ne mara kyau, wanda bai dace ba ga Maza, ko da namiji zai kara aure to cin fuska ne ya ringa waya da budurwarsa ta waje a gaban matarsa, ko ma hakan ne to ya zama an saka ranar aure, kuma maganar ta zama me amfani ba wai hirar soyayya ba. Abin da zan kira hakan shi ne cin fuska da neman rigima, kuma laifin namiji ne. Shawarar da zan ba ta shi ne; ta koma gidan mininta don shi ne rufun asirinta ko ‘yar wa ce ce ita, sannan tayi hakuri da shi in hakan halinsa ne, kowanne namiji da nasa kalar matsalar, kuma a ja masa kunne shi ma. Sabida zaman gidan miji ya fi zaman zawarci, idan kuma akwai yara tsakaninsu to ba za su sami kulawa ba kamar mahaifiyarsu tana tare da su. Shawarar da zan ba mazan ita ce, su ji tsoron Allah su daina, sannan kuma su kiyaye hakkokin iyalensu kada su yi abin da zai batawa matansu rai da gangan, sannan mata suna da kishi dole ne su ji bacin rai yayin da mijinsu ke waya da wata a waje, duk da sun san zai kara auren. Sannan ko don zaman lafiyar gidan ma bai kamata su rinka yin hakan ba.
Sunana Safiyya Mustapha Mu’az daga Gurin Gawa:
A gaskiya sam! hakan bai kamata ba, bai kamata ace namiji me iyali ya zauna a gidansa tare da iyalinsa kuma ya kama kiran ‘yan mata a gaban matarsa ba. Sabida ba za ta ji dadi ba, kuma hakan bai kamata ba, in ace ma yana son ya kira ta to tun a waje sai ya kira ta, amma da zarar ya shigo gidansa to wannan lokacin matarsa ne. Shawarar da zan bata ta koma gidan mijinta amma fa ta gyara zamantakewar Auransu tsakaninta da mijinta. Shawarata ga masu irin wannan dabi’ar suyi hakuri su daina sam hakan bai dace ba kamata yayi idan matarka bata kyautata maka ko tana maka wani da baka so ka sameta kayi mata bayani a nutse akan ta gyara, idan kuma kana son yin waya da budurwarka to kayi a waje idan ka fita, amma idan ka dawo gidanka ka sani wannan lokacin matarka ne, bai kamata ka zo kana waya da budurwarka a gaban matarka ba, hakan bai dace ba gaskiya.
Sunana Ibraheem Ismail Ibrahim daka Jihar Kano:
Gaskiya bai kamata ba, rashin sanin ya kamata ne, kuma duk abin da ka yi wa ‘yar wani kai ma sai an yi wa ‘yar ka, ko ‘yar uwarka, rashin adalci ne. Laifin na namiji ne ta ci gaba da yi masa addu’a har Allah ya shirye shi ta koma kar ta ki komawa bayan wahala sai dadi, mahakurci mawadaci.
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Gaskiya wanan rashin adalci ne ga mata, kuma bai kamata ba hakan, zai iya sa matarka ta raina ka ma. Gaskiya wani lokacin lafin mazan ne domin ba sa iya zama da matansu ba tare da sun kula wasu matan na waje ba, wani lokacin kuma na matan ne sabida wasu ba sa kula da mazajen yadda ya kamata, wasu kuma ba laifinsu bane suna iyakar kokarinsu. Shawarata a nan ita ce; ta gyara zamantakewarta da mazan za ta ga canji kuma ta koma dan yanzu zawarci ba shi da dadi, shi kuma namiji in laifi matar sa ta yi mai sai ya zauna da ita su sasanta da sakin auren bashi da dadi na gode ina yi muku fatan Alheri.
Sunana Nafisa Usman Muhammad daga Jihar Kano:
Eh! gaskiya ana samu sosa masu irin wannan dabi’a. Ba komai bane illah rashin adalci, kuma dukkansu suna da laifi. Shawara ta koma, abin da ya sa, komai ka gani a cikin zamantakewa hakuri ake yi da shi. Gaskiya hakan bai kamata ba ko da ace kana yi ka gama kafin ka shiga gida.
Sunana Aminu Abdullahi Umar daga Jihar Kano:
Gaskiya hakan ba dai-dai bane ya kamata a bawa kowa hakkinsa a zamantakewa musamman rayuwar aure. Hakan zalunci ne kuma laifin mijin ne, ta koma gidan mijinta amman magabata su shiga tsakaninsu saboda gujewar abu makamancin haka. Shawara duk namiji mai irin wannan hali dai yana shiga hakkin matarsa, kuma shi ma yana da ‘ya‘ya sannan yana da damar fita yai wayar sa ya dawo ba wanda ya sani hakalin kowa a kwance.
Sunana Yakubu Obida Unguwar Farawa Jihar Kano Karamar Hukumar Kumbotso:
Gaskiya wannan salon iskanci ne gaskiya, kuma bai kamata ba, domin wannan ba adalci bane, idan kai kana ganin kai ba komai bane to gaskiya hakan na da ciwo wanda ba lallai ka fahimta ba, kuma wannan abun da ke faruwa kenan kuma wannan ba adalci bane, ya kamata ay mata kara in ka zo gida, a waje kai rashin mutuncinka a gida ka bata hakkinta. Gaskiya kowane bangaren zai iya yuyuwa da nasa lefin ko dai ita matar ta mai laifi ko kuma shi yake nema ya bata ta, ko kuma akwai abun da yake faruwa a tsakaninsu ko tai masa lefi sai ya bujire ya ga cewar bara kowa kawai yai abunda yake so, amma duk yadda ake ciki dai in daya yayi wa daya lefi to ayi hakuri. Shawarar da zan bata gaskiya hakuri shi ne farko, na biyu ta koma tayi zaman hakuri, idan tana da yara tai zaman yaranta sai kuma ta bar wa Allah komai, Allah shi yai komai kuma shi zai iya can za komai a lokacin da ya ga dama. Gaskiya a gaskiya Maza masu wannan dabiar Ina rokar su da duk yanayin da muka tsinci kan mu ko da mune da gaskiya mu kasance masu hakuri, saboda bayan aure soyayya na iya canzawa, so duk abun da mace ta yi maka ayi hakuri kuma a sasanta a fahimci juna.