matashin dan wasan gaban Ingila dake buga kwallo a kungiyar kwallon kafar Arsenal ta Firimiya Lik ya rattaba hannu akan karin kwantiragin shekaru hudu a Arsenal wanda zai barshi a kungiyar har zuwa 2027
Saka wanda ya zura kwallaye 14 kuma ya taimaka aka jefa 11 a kakar bana ya buga wa Arsenal Wasanni 178 a shekarun da yayi a kungiyar.
Dan Shekaru 21 Saka yana daga cikin zakakuran matasan yan kwallo da tauraruwarsu ke haskawa a nahiyar turai,ya bayyana cewar yana matukar jin dadin zamansa a Emirates Stadium kuma yana kyautata zaton akwai abinda yake bukata na zama zakaran kwallon Duniya Idan yana Kungiyar.