Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci zama na farko na kwamitin koli a fannin aikin tantance alkaluma, na jam’iyyar kwaminis ta kasar karo na 20 da maraicen yau Talata 23 ga wata, inda ya gabatar da muhimmin jawabin dake jaddada cewa, a yayin da kasar Sin take kokarin raya kanta, da farfado da al’ummun ta baki daya, aikin tantance alkaluma na daukar babban nauyi.
Xi ya jaddada cewa, ya dace a sa ido kan bunkasar tattalin arziki, da maida hankali kan babban nauyi da manyan sana’o’i, ta yadda aikin tantance alkaluma zai kara taka rawa ta musamman, a fannin yi wa jam’iyyar kwaminis kwaskwarima da kanta. (Murtala Zhang)