Gwamnatin Jihar Kano ta dauki karin masu share tituna don samar da tsafftacen muhalli a fadin jihar.
Kwamishinan Muhalli na jihar, Dakta Kabiru Getso, ya sanar da haka bayan da ya jagoranci kwamitin gwamnatin jihar na masu lura da yadda ake gudanar da shirin tsaffatace muhalli da ake yi duk karshen wata.
Ya ce, za a tura sabbin wadanda aka dauka titunan BUK, Kabuga- Danagundi, Gandun Albasa, Zoo road, Court road, Aminu Kano road da kuma Maiduguri road da sauransu.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa, kwamitin nasu ya ji dadin yadda aka tsaftace wuraren da suka ziyarta, ya kuma yaba wa al’umma a kan yadda suke bayar da hadin kai a duk ranar tsaftace muhalli da aka ware.
Kwamishinan wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da tsaffatace muhallin ya gargadi al’umma a kan zuba shara a kan tituna.
Kamfanin Dillancin Labarai ya bayyana cewa, kotun tafi-da-gidanka ta daure mutum 60 da suka karya dokar tsaftace muhalli inda aka yi musu tarar Naira 119,500.