Ƙungiyar siyasa ta ‘Ah-lulbayt Political Forum’, wacce ke karkashin kungiyar mai akidar shi’a reshen Jihar Kaduna, ta ƙara jaddada goyon bayanta ga sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu, domin nuna matuƙar damuwa da nuna rashin jin daɗi kan aikin rusau da gwamnatin Jihar Kaduna ke ci gaba da yi, musamman kan ‘yan kungiyar da sauran ɗaiɗaikun mutane.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Sulaiman Muhammad ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, 26 ga watan Mayu, 2023, inda ya ce, “Haƙiƙa bai dace ba domin hakan na iya wargaza zaman lafiya da jihar ke samu, musamman ganin yadda muke kan hanyar samun sauyi ta dimokuraɗiyya.”
Muhammad ya kara da cewa, “Muna kara kira ga gwamnati da ta mutunta tare da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasarta ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba, kamar dai yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada.”
“Muna kuma kira ga ɓangarorin da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu, ka da su ɗauki doka a hannu, su nemi haƙƙinsu ta ɓangaren doka.
“Daga ƙarshe muna kira ga gwamnati mai jiran-gado da ta binciko hanyoyin magance rikice-rikicen da suka addabi jihar, musamman tattaunawa da kuma mai da hankali wajen warware matsalolin wannan yanayin,” in ji Muhammad.