Sakamakon wani nazari ya bayyana cewa, galibin kamfanoni masu jarin waje dake gudanar da harkokinsu a kasar Sin, sun yabawa yanayin kasuwanci mai kyau na kasar Sin, tare da bayyana kwarin gwiwar da suke da shi kan kasuwar kasar.
Wang Linjie, jami’i a hukumar bunkasa cinikayya da kasashen ketare ta kasar Sin (CCPIT), ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Talata cewa, kaso 97 na kamfanonin da aka nazarta, sun ce sun gamsu da manufofin kasar Sin na bunkasa jarin waje da aka gabatar daga farkon rubu’i na 4 na karshen bara, zuwa yanzu.
A cewarsa, kamfanonin kasashen waje suna da yakini kan makomar kasuwar kasar Sin yayin da kasar ke ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci da bunkasa ayyukan masana’antu da tsarin samar da kayayyaki da saukaka cinikayya tsakanin kasa da kasa. (Fa’iza)