Gwamnatin jihar Zamfara ta yi fatali da wani labari da aka yada wa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa Gwamnan Jihar, Dauda Lawal, ya bayyana kadarorinsa na Naira Tiriliyan 9.
Gwamnatin cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Juma’a a Gusau, ta bayyana labarin a matsayin kage da karya da aka tsara domin kawar da sabuwar gwamnati daga tafarkin ceto Zamfara.
- INEC: Dauda Lawal Ya Karbi Takardar Shaidar Lashe Zaben Gwamnan Jihar Zamfara
- Gwamnan Zamfara Ya Yi NaÉ—e-naÉ—en WaÉ—anda Za Su Taimaka Masa
Sanarwar ta ce ci gaba da cewa kagaggen labari ne daga wadanda suka fadi zabe suke kitsa shi, kamar yadda suka yi a lokacin yakin neman zabe.
Sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali wajen ganin ta zo da bukatun da ake bukata a harkokin gudanar da mulki a jihar domin gudanar da ayyukanta.