Kasar Sin ta bayyana matukar rashin gamsuwa tare da korafinta ga kasar Amurka dangane da wata yarjejeniyar cinikayya da aka rattaba hannu a kai tsakanin Amurkar da yankin Taiwan a jiya Alhamis.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana haka, yayin taron manema labarai na yau Juma’a.
A cewar Mao Ning, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na musaya tsakanin yankin Taiwan da kasashen dake da dangantakar diflomasiyya da kasar Sin, ciki har da shawarwari da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi a hukumance. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp