Sassa daban daban daga jihar Xinjiang mai cin gashin kai ta Uygur ta kasar Sin, sun yi Allah wadai da dokar da Amurka ta kafa mai suna wai “ Dokar magance aikin tilas ta Uyghur,” inda suka bayyana cewa, matakin wani yunkuri ne na lahanta moriyar wasu ba tare da samun amfani komai ba ga ita kanta, kuma matakin ya kawo illa matuka ga muhallin kasuwancin kasa da kasa.
Xu Guixiang, kakakin gwamnatin jihar ya bayyana a taron manema labarai a ranar Juma’a cewa, matakin da Amurka ta dauka na haramta sayen kayayyakin yankin Xinjiang tamkar wani fashi a bayyane, kuma wani mataki ne na nuna danniya, da ra’ayin yakin cacar baka.
Ya kara da cewa, matakin wata babbar barazana ce ga tsaron tsarin masana’antu da kuma tsarin samarwa da kayayyaki na kasa da kasa, kuma yayi matukar haifar da koma baya wajen tabbatar da adalci a muhallin kasuwancin kasa da kasa.
Shi ma Shang Xiaoke, jami’in kungiyar ma’aikatan kwadago na wani kamfanin hada sinadarai na Xinjiang ya ce, wannan batu da ake kira wai ‘aikin tilas’ kawai wani rashin tunani ne.’
A cewar Hamiti Abdurehei, wani mai bincike a cibiyar nazarin cigaba ta Xinjiang, tsarin dokokin kasar Sin ya samar da gagarumar kariya ga hakkokin ma’aikata da moriyarsu, kuma ma’aikatan dukkan kabilun yankin Xinjiang suna da ‘yancin zabar irin sana’ar da suke so, ko kuma wuraren da suke sha’awar yin aiki.(Ahmad)