Gwamnatin Jihar Taraba ta sake jadadda aniyarta na kawo karshen cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) nan da zuwa 2030.
Wannan na zuwa ne ta hannun Hukumar Da Ke Dakile Cutar a Jihar.
- An Tsinci Wani Yaro An Kwakwule Masa Idanu A Bauchi
- 2023: Kwankwaso Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Watsi Da APC Da PDP
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin kokarin da ta ke yi duk sati kan mayar da hanklai ta hanyar saduwa a jihar don dakile yaduwar cutar da kuma yakar cutar tarin fuka a tsakanin marayu da yara masara galihu.
A daidai lokacin hada wannan rahoton, masu fama da cutar mai karya garkuwar jiki a jihar sun haura mutum 36,396 ne ke ci gaba da karbar magani, inda daga cikin wannan adadin, an duba lafiyar mutane 20,200.
Har ila yau, daga cikin adadin mutanen a kananan hukomin jihar, guda 2,156 an tabbatar da sun kamu da cutar, inda a nazarin da aka yi makaon da ya wuce, an tabbatar da mutane 77 da suka kamu da cutar.
Bugu da kari daga cikin adadi guda 359 da aka yi wa gawajin cutar yara ne ‘yan kasa shekaru 14
Da ya ke yin jawabi, Darakta-Janar na Hukumar, Dakta Garba Danjuma, ya shelanta cewa, burin gwamnatin jihar shi ne, ta dakile cutar a jihar kafin zuwan shekarar 2030, musamman don ta tabbatar babu wai da ya mutu a dalilin kamuwa da cutar.