Mai magana da yawun rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin PLA, babban kanar Shi Yi ya yi tir da yunkurin tunzura jama’a da jirgin ruwan yaki mai dauke da makamai masu linzami mai suna Chung-Hoon (DDG 93) da jirgin ruwan yaki mai ajin Halifax mai suna Montreal (FFG 336) suka yi wajen ratsa mashingin takun Taiwan a ranar Asabar.
Shi Yi ya bayyana a cikin wata rubutacciyar sanarwa cewa, kasar Sin ta yi tir da wannan mataki na takala. Yana mai bayyana cewa, rundunonin sojan ruwa da na sama dake gabashin kasar, sun rika sanya ido kan jiragen ruwan kasashen Amurka da Canada a duk tsawon lokacin, tare da kula da lamarin bisa doka da kuma fasaha.
Shi ya yi nuni da cewa, da gangan kasashen da abin ya shafa ke neman tada tarzoma a mashigin tekun Taiwan, da yin zagon kasa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tare da aika sakonnin da ba su dace ba ga ‘yan awaren Taiwan.
Kakakin rundunar ya jaddada cewa, rundunar sojin PLA da ke yankin gabashin kasar, za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, da daukar dukkan matakan da suka dace bisa doka, wajen dakile duk wata barazana da tunzura jama’a, da tabbatar da kiyaye ikon mulkin kan kasa, da tsaro, da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Ibrahim)