Wata kotun tarayya ta dakatar da kungiyoyin kwadago (NLC) da ta ‘yan kasuwa (TUC) shiga yajin aiki a ranar Laraba.
Mai Shari’a O.Y. Anuwe ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin kuma ya dage zaman cigaba da sauraron karar zuwa 19 ga watan Yuni.
Kungiyoyin, tun a baya sun yi yunkurin shiga yajin aiki a fadin Nijeriya kan kudurin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur baki daya.
Cikakken rahoto na zuwa…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp