Wasu sabbin alkaluma da shafin yanar gizon Caixin ya fitar yau Litinin sun nuna cewa, ayyukan samar da hidima na kasar Sin sun sake farfadowa sosai a watan Mayu, yayin da ma’aunin sayayya a fannin (PMI) ya karu zuwa kashi 57.1 cikin 100 daga kashi 56.4 a cikin watan Afrilu.
Karuwar da aka samu a bangaren samar da hidimar, ta ci gaba har tsawon watanni biyar a jere kuma ta karu cikin sauri a karo na biyu a cikin watan Mayu tun daga watan Nuwamba na shekarar 2020. (Mai fassarawa: Ibrahim)