Wakilai daga kasashen Afirka 50 da kungiyoyin kasa da kasa 8, sun yi rajistar halartar bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na uku, wanda zai gudana daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.
Shugaban sashen kasuwanci na lardin Hunan Shen Yumou, ya shaidawa wani taron manema labarai Talatar nan cewa, yayin baje kolin mai taken “Samun bunkasuwa don makoma ta bai daya”, za kuma a gabatar da ayyuka sama da 40 irin daban-daban, wadanda suka hada da samar da ababen more rayuwa maras gurbata muhalli, da harkokin kwastan da killacewa, da magunguna da kiwon lafiya, da kayayyakin noma da abinci, da yankunan masana’antu, da ilimin sana’a da sauran fannoni.
Kasashen da za su halarci bikin baje kolin sun hada da Benin, da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da Madagascar, da Malawi, da Morocco, da Mozambique, da Najeriya da kuma Zambia. (Mai fassarawa: Ibrahim)