Shugaba Bola Tinubu ya umurci Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ta fara aiki don nemo mafita ta yadda ‘yan Nijeriya za su samu saukin radadin cire tallafin man fetur.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ne ya bayyana haka bayan ya jagoranci wata tawagar manyan ‘yan kasuwar man fetur a ziyarar ban girma da suka kai wa shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan ganawar, ya ce, ’yan kasuwar sun kawo ziyarar ne fadar shugaban kasa don nuna goyon bayansu ga Shugaban kasa kan babban matakin da ya dauka na kawo karshen biyan tallafin man fetur.
Ya yi nuni da cewa, matakin da Tinubu ya dauka, ya nuna himmarsa da jajircewarsa wajen kawar da nauyin da ya addabi kasar nan tsawon shekaru da dama.
Gwamnan ya ce, duk da cewa, za a samu rashin jin dadi a bangaren jama’a, amma a karshe matakin zai yi tasiri domin babu wata nasara sai an yi juriya.
‘Yan kasuwar sun bayyana aniyarsu ta ba da gudummawar motocin bas guda 50 zuwa 100 don rage wa jama’a radadin damuwa sanna kuma sun yi fatan sauran kungiyoyin kamfanoni su ma za su bada tasu gudunmawar.