Bankin duniya ya fitar da sabon rahoton hasashen tattalin arzikin duniya a ranar 6 ga watan Yuni, inda ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai bunkasa da kashi 2.1% a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 0.4% bisa kiyasin da aka yi a watan Janairu, amma duk da haka bai kai na shekarar 2022 wanda ya kai kashi 3.1% ba.
Tattalin arzikin kasar Sin kuma zai bunkasa ya karu da kashi 5.6 cikin 100 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 1.3% bisa hasashen bankin a Janairu.
Rahoton ya yi nuni da cewa har yanzu tattalin arzikin duniya yana cikin wani yanayi maras tabbas a dalilin tasirin annobar COVID-19, rikicin Rasha da Ukraine, da kuma tsauraran manufofin kudi.
Hauhawar kudin ruwa a Amurka cikin sauri yana haifar da manyan ƙalubale ga kasuwanni masu tasowa da ƙasashe masu ci gaba, wanda ke haifar da yuwuwar matsalar hada-hadar kuɗi.(Yahaya)