Alkaluman da ma’aikatar ilimi ta kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa dalibai miliyan 12.91 ne suka yi rejistar rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandare domin shiga jami’a, wadda ake kira da Gaokao, adadin da ya karu da 980,000 a kan na bara, inda ya zama mafi yawa a tarihin jarrabawar Gaokao ta kasar. An kaddamar da jarrabawar ne a jiya Laraba.
Ma’aikatar ta yi kira ga hukumomi a yankuna da su tabbatar da jarrabawar ta wakana cikin aminci da adalci.
Kimanin dalibai 10,000 masu bukata ta musamman ne aka samar musu da wurare na musamman a fadin kasar domin tabbatar da sun samu damar rubuta jarrabawar. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp