Hukumar tsaron farin kaya (DSS), ta ce gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele, ba ya hannunsu.
Da yake mayar da martani ga rahotannin da ke cewa hukumar ta DSS ta kama Emefiele a daren Juma’a jim kadan bayan dakatar da shi daga aiki a matsayin gwamnan babban bankin na CBN, mai magana da yawun hukumar DSS, Dr Peter Afunanya ya ce “a halin yanzu Emefiele ba ya tare da DSS.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin Nijeriya ta dakatar da gwamnan CBN, Emefiele,
Baya ga dakatar da shi daga ofis don gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge kamar yadda shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana, hukumar DSS a farkon wannan shekarar, ta zargi Emefiele da wasu zarge-zarge da suke da alaka da amfani kudade wajen ta’addanci.
Hukumar ta DSS ta ce tana tuhumar gwamnan CBN da aka dakatar da zargin hannu wajen samar da kudaden ta’addanci kuma dole ne ya amsa laifin da ake zarginsa da shi.
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya gano wasu ayyukan ta’addanci da suka hada da ba da kudade, ayyukan zamba da Emefiele ya aikata da kuma shigar sa cikin laifukan tattalin arziki da suka shafi tsaron kasa.