A ci gaba da bikin fina finai na kasa da kasa na Shanghai karo na 25, a jiya Asabar, an kaddamar da makon fim na ziri daya da hanya daya a birnin Shanghai.
Mashirya bikin dai sun ce akwai jimillar fina finai 20 na gida da na ketare, wadanda za a tantance yayin bikin na bana. A cikin su akwai guda 8, da suka hada da fim din “Absence”, da fim din kasar Hungary mai suna “Six Weeks”, wadanda za su yi takarar lashe manyan lambobin karramawa a bikin na wannan karo.
Tauraron fina finan kasar Sin, kuma jakadan yayata makon fim na ziri daya da hanya daya na bana Lei Jiayin, ya ce akwai mashirya fina finai daga sassan duniya daban daban, da suka tsara fina finai masu kayatarwa da ke fayyace tarihi na yanzu, da ma na nan gaba, game da “Ziri daya da hanya daya”.
A bana ne dai ake cika shekaru 10 da fara aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, kuma ita ce shekara ta 5, ta fara gudanar da bikin gamayyar masu fina finai na ziri daya da hanya daya. Gamayyar da a yanzu ta samu sa hannun abokan hulda 55 daga sassan duniya daban daban.
Makon fim na ziri daya da hanya daya, zai gudana ne har zuwa ranar 18 ga watan nan. Kuma baya ga haska fina finai, zai kunshi karin wasu ayyuka daban daban, kamar tarukan karawa juna sani, da dandaloli da gasanni. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp